Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF), Ibrahim Gusau, ya yi murabus daga mukaminsa.
Gusau ya sanar da murabusin sa a ranar Alhamis a wata ganawa da manema labarai a Abuja, hakan ya kawo karshen mulkin sa a harkokin gudanar da kwallon kafa a Najeriya.
Murabusin sa ya zo ne cikin lokacin da ake ci gaba da suka ga NFF saboda karuwar koma-bayan da tawagogin kasar ke fuskanta.
Wannan lamari ya biyo bayan gazawar Super Eagles da Super Falcons wajen samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026 da 2027. Wannan ya kara matsa lamba kan shugabancin hukumar.













































