Sakataren NLC Emmanuel Ugboaja ya rasu

Emmanuel Ugboaja 750x430

Emmanuel Ugboaja, Sakataren Janar na Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), ya rasu yana da shekara 60 bayan ya yi fama da dogowar jinya.

Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, babu cikakken bayani game da rasuwar sa.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ne ya sanar da mambobin Majalisar Zartarwa ta Kasa labarin, inda ya karanta wasika daga iyalin marigayi Sakataren Janar ga wakilai da ke taro yanzu a Enugu, Jihar Enugu.

Ugboaja, tsohon dan kungiyar kwadago kuma lauya, ya rike mukamin a NLC tun daga watan Agusta 2019, lokacin da Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da nadin sa a taron da aka yi a Kano, inda ya gaji Peter Ozo-Eson da yayi ritaya.

A matsayin Sakatare Janar, Ugboaja shi ne ya ke tafiyar da tsarin gudanarwa da dabaru na NLC, daidaita kungiyoyin da ke karkashin NLC, gudanar da harkokin aiki, tattaunawa da gwamnati da masu daukar ma’aikata, tsara manufofi da kuma tara ma’aikata, yayin da Shugaba Ajaero ke zama fuskar siyasar kungiyar.

Gogewarsa a harkokin aiki ta taimaka wajen jagorantar wasu manyan rikice-rikicen kungiyar kwadago da gwamnati, gwajin shi na farko bayan ya hau mulki a 2019 shi ne shiga tattaunawa kan aiwatar da sabon karin albashi na N30,000, lamarin ya kai kungiyar kwadago kusa da yajin aiki kafin a cimma matsaya.

Ya ci gaba da kasancewa babban mutum a harkokin kungiyar kwadago da gwamnati a shekarun baya, inda a watan Afrilu 2026, ya rattaba hannu kan umarnin NLC da ya bukaci ma’aikata a jihohin da ba su cika aiwatar da Dokar Sabon Karin Albashi ta 2024 ba da su gudanar da zanga-zanga a titi a ranar Ma’aikata ta Duniya, 1 ga Mayu, wannan ya nuna rawar da yake takawa wajen juya manufofin kungiyar zuwa aiki a fadin kasar.

An haifi Ugboaja a ranar 15 ga Mayu, 1966, ya karanta shari’a a Jami’ar Calabar, inda ya kammala a 1987, ya kuma yi aikin lauya na tsawon shekaru hudu kafin ya shiga harkokin kungiyar kwadago a 1993, wannan matakin ya sa ya zama, bisa tarihin NLC, dan Najeriya na farko lauya da ya yi aiki na cikakken lokaci a kungiyar kwadago.

Ya fara ne da Kungiyar Ma’aikatan Kasan Sinadari, Takalma, Roba, Fata da Kayayyakin da Ba Karfe ba (NUCFRLANMPE), wata kungiya da ke karkashin NLC, inda ya kai ga zama Sakataren Janar na kungiyar daga 2000 zuwa 2005.

Bayan haka ya fadada aikinsa daga 2006 zuwa 2009, ya yi aiki a Alliance for Credible Elections, wata kungiya ta farar hula da ke kula da harkokin zabe daga nan ya shiga sakatariyar NLC a 2009.

Ugboaja ya kuma wakilci kungiyar kwadago a manyan tarukam sauya tsarin mulki guda biyu: Taron Sauya Tsarin Mulki da Siyasa karkashin Shugaba Olusegun Obasanjo a 2005 da kuma Taron Sauya Kundin Tsarin Mulki karkashin Shugaba Goodluck Jonathan a 2014.

Kafin ya zama Sakatare Janar, ya yi aiki a NLC a matsayin Babban Mataimakin Sakatare Janar da kuma Shugaban Sashen Harkokin Aiki da Shirya Kungiya, wadannan mukamai ne suka shirya masa hanya zuwa babban mukamin da ya samu a 2019 bayan an zabe shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here