Hukumar Jin Dadin Alhazzai ta Jihar Kano ta sanya ranar 31 ga watan Agusta a matsayin ranar karshe ta mika fasfo din maniyyata da ke son halartar aikin Hajjin shekarar 2026.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi, ya sanya wa hannu a ranar Talata a Kano.
“Ranar karshe ta dorawa bayanan fasfon maniyyata a na’ura tana nan a 31 ga watan Agusta,” in ji Babban Daraktan.
Ya yi kira ga sama da maniyyata 700 wadanda aka riga aka dauki hotunan yatsunsu da su gaggauta karbar fasfo din na su daga ofishin Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa don mika wa ga hukumar alhazzai ta jiha.
“Fasfon maniyyata wadanda aka riga aka dauki bayanansu sun riga sun fito, kuma a shirye suke don karba.
Kamata ya yi maniyyata su karbi na su ba tare da bata lokaci ba, domin baiwa hukumar damar dora bayanansu a babban shafinta da kuma fara shirye-shiryen da suka dace na aikin Hajji,” in ji shi.
Ya yi gargadin cewa rashin karba da kawo fasfo din akan lokaci na iya shafar kammala takaddun maniyyata da sauran shirye-shiryen aikin Hajji cikin lokaci.
Ibrahim Matawalle ya jinjinawa hukumar NIS bisa hadin kai da tallafin da take bayarwa wajen gudanar da aikin tantance fasfo na maniyyatan jihar cikin nasara.
Babban Daraktan ya yi kira ga dukkan maniyyata da su bi wannan doka ta ranar karshe da aka sanya, sannan su kammala takaddunsu cikin hanzari. (NAN)













































