Eid-el-Maulud: Shettima ya bukaci ‘Yan Najeriya da su karfafa dankon hadin kai

Kashim Shettima sabo 750x430 (2)

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yi kira gayan Najeriya da su karfafa dankon zumuncin da ke hada kansu, su yi watsi da kowane nau’in kiyayya, rarrabuwar kawuna, rashin jituwa, sannan su taimaki marasa karfi.

Shettima ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a cikin sakonsa na taya murna ga al’ummar Musulmi da daukacin ‘yan Najeriya bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi.

A cewarsa, bambance-bambancen da ke tsakanin ‘yan Najeriya na ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan karfi da ikon kasar.

Don haka, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da gina kasar da mutanan kowane addini da kabila za su iya zama tare cikin lumana, mutunci da girmama juna.

Mataimakin shugaban kasar ya mika sakon murna ta musamman ga al’ummar Musulmi da daukacin ‘yan Najeriya yayin biki na zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi).

Ya bayyana cewa rayuwar Annabi ta kasance madubin koyi madawwami wajen tausayi, tawali’u, adalci, hakuri da hidimawa bil’adama.

“Ya koyar da mu cewa tabbataccen karfi yana cikin juyayi da tausayi, kuma dole ne jagoranci ya ginu a kan adalci, sannan ana nuna kyawun addininmu ne ta hanyar yadda muke mu’amalanci juna.

“A daidai lokacin da kasarmu ke ci gaba da samun dorewar bunkasar tattalin arziki a karkashin Tsarin Sabunta Fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, dole ne wadannan dabi’u su zaburar da mu.

“Wadannan dabi’u na bukatar su zaburar da mu domin mu karfafa dankon zumuncin da ke hada mu, mu kula da marasa karfi, sannan mu yi watsi da kowane nau’i na kiyayya, rarrabuwar kawuna, da rashin juriya,” in ji shi.

Haka itama, mataimakin shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su tuna da mabukata, sannan su nuna kyautatawa ga makwabtansu da ma al’ummominsu baki daya.

“Manufar wannan biki ba wai kawai tunawa da ranar ba ne, a’a, har da aiwatar da koyarwar Annabi a cikin rayuwarmu ta yau da kullum.

“Yayin da muke gudanar da wannan biki, ina kalubalantar ‘yan Najeriya da su tuna da wadanda ke cikin rashi, sannan su yawaita kyautatawa ga makwabta da al’ummominmu.

“Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya karbi addu’o’inmu, ya samar da dawwammen zaman lafiya da arziki a kasarmu, sannan ya shiryar da mu baki daya a kan tafarki madaidaci.” (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here