Ranar Juma’a ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a zaben gwamnan jihar. An gudanar da zaben jihar ne a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Dan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sadique Abubakar, ya daukaka karar biyo bayan hukuncin kotun kararrakin zabe da ta tabbatar da nasarar Mohammed.
Mai shari’ar kotun ya karanta hukuncin ne a kan korafin da mai daukaka karar ya shigar gaban kotun.
A kara ta daya, mai shigar da karar ya roki a soke zaben saboda ba a cike fom da takardun da aka yi amfani da su a zaben yadda ya kamata ba.
Kotun ta yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da karar ya gaza gabatar da hujjoji kan wannan zargi.
Kotun ta ce wanda ya shigar da karar ya kasa bayyana akwatunan zaben da aka aikata laifukan da ya ke zargi, kuma ya kasa bayyana abin da aka cire daga fom din.













































