Jami’ar Azman Da Wasu 37 Sun Samu Lasisin Fara Aiki

National Universities Commision NUC
National Universities Commision NUC

Jami’ar Azman mai zaman kanta da aka kafa a Jihar Kano da wasu sabbin jami’o’i masu zaman kansu a Najeriya na karbar lasisinsu na fara aiki a ranar Juma’a

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) na damka wa Jami’ar Azman da Jiami’ar El-Amin da ke Minna a Jihar Neja da sauran 37 lasisinsu ne a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Shugaban Kwamitin Amintattu na Jami’ar El-Amin, mallakin kamfanin El-Amin Nigeria Limited, shi ne tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Takwaransa na Jami’ar Azman kuma shi ne Barista Ado Muhammad Ma’aji, kuma jami’ar mallakin Rukunin Kamfanin Azman ce.

Kamfanin Azman ya fara ne da harkar man fetur daga baya ya shiga harkar sufurin jiragen sama kafin yanzu su fara harkar jami’a.

Sunayen jami’o’in da aka bawa lasisins:

Rayhaan University, Kebbi; Muhammad Kamalud University Kwara; Sam Maris University, Ondo; Aletheia University, Ago-Iwpye Ogun; and Lux Mundi University Umuahia, Abia.

Maduka University, Ekwegbe, Enugu; PeaceLand University, Enugu; Amadeus University, Amizi, Abia ; Vision University, Ikogbo, Ogun; and Azman University, Kano.

Huda University, Gusau, Zamafara; Franco British International University, Kaduna; Canadian University of Nigeria, Abuja; Miva Open University, Abuja FCT; and Gerar University of Medical Science Imope Ijebu, Ogun.

British Canadian University, Obufu Cross River; Hensard University, Toru-Orua, Sagbama, Bayelsa; Phoenix University, Agwada, Nasarawa; Wigwe University, Isiokpo Rivers; da kuma Hillside University of Science and Technology, Okemisi, Ekiti.

Raguwar Jami’o’in sune University on the Niger, Umunya, Anambra, Elrazi Medical University Yargaya University, Kano, Venite University, Iloro-, Ekiti , Shanahan University Onitsha, Anambra , The Duke Medical University, Calabar, Cross River, Mercy Medical University, Iwo, Ogun, Cosmopolitan University Abuja da kuma Iconic Open University, Sokoto.

Sauran su ne West Midlands Open University, Ibadan, Amaj University, Kwali, Abuja, Prime University, Kuje, FCT Abuja, College of Petroleum and Energy Studies, Kaduna, Jewel University, Gombe, Nigerian University of Technology and Management, Apapa, Lagos, Al-Muhibbah Open University, Abuja and Al-Bayan University, Ankpa, da kuma Kogi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here