Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce da sun hadu da takwaransa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a Villa da ya dalla masa mari.
Dr Ganduje ya bayyana haka ne da yammacin Juma’a a Fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ya ce ya je Villa ne kai karar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf kan yadda yake rushe gine-gine a wuraren da shi Gandujen ya bayar a zamanin mulkinsa.
Ya na cikin Villa ne kuma Sanata Rabiu Kwankwaso suka shiga tattaunawar sirri da shugaban kasa Bola Tinubu.
Wannan ce ta sa Dr Ganduje ya bayyana takaicinsa da zuwan Sanata Kwankwason.
“Bamu hadu da shi ba, amma da na gan shi da zan iya kantsa masa mari saboda barnar da ya kawo a Kano” in ji Ganduje.
(Aminiya )