Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Samaila Bagudu, a garinsu Bagudu da ke ƙaramar hukumar Bagudu.
Wata majiya ta bayyana cewa ’yan bindigar sun kutsa cikin garin Bagudu a ranar Juma’a da dare suna harbe-harbe ba kakkautawa.
Majiyoyin sun ce an yi garkuwa da mataimakin shugaban ne bayan ya kammala sallar Isha’i kuma yana komawa gida daga masallaci.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels.
Ai dai duk ƙoƙarin samun karin bayani daga rundunar ’yan sandan jihar Kebbi game da lamarin hakan bai samu nasara ba.
Karin bayani na nan tafe……













































