Durbin Kano, Mohammed Koguna ya rasu yana da shekaru 87

alhaji m h koguna 300x300 1

Fitaccen ɗan kasuwa kuma mai rike da sarautar gargajiya a masarautar Kano, Dakta Mohammed Hassan Koguna wanda aka fi sani da Durbin Kano, ya rasu yana da shekaru 87 bayan fama da jinya a asibiti da ke birnin tarayya Abuja.

Ɗansa, Hon. Nasiru H. Koguna, ne ya sanar da rasuwar mahaifinsa a ranar Asabar cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta bayyana cewa za a yi sallar jana’izarsa da ƙarfe goma na safe a yau Asabar a fadar sarkin Kano da ke ƙofar kudu.

Koguna ya kasance shugaban kamfanin Kamfanonin Koguna da Babura Insurance Brokers Limited, kuma tsohon jakadan girmamawa na Jamhuriyar Turkiyya mai kula da jihohi goma sha tara na Arewacin Najeriya.

Ya kuma yi aiki a matsayin Darakta mai ba da shawara a Kamfanin Jiragen Sama na Biritaniya Caledonian Airways daga shekarar 1982 zuwa 1985, da kuma darekta a Kamfanin Inshora na Kapita daga 1985 zuwa 1996.

Haka kuma, ya rike mukamin shugaban hukumar Kamfanin Ma’aunin Wutar Lantarki daga 1985 zuwa 2001, da kuma Kamfanin Inshora na Continental Reinsurance Ltd daga 1985 zuwa 2001.

Ya kasance mamba a Kwamitin Afuwar Jiha ta Kano daga 1970 zuwa 1975, da kuma a Hukumar Gudanar da Otal-Otal na Jihar Kano daga 1976 zuwa 1979, tare da zama guda daga cikin ɗan majalisar Masarautar Kano daga 1976 zuwa 1977.

Koguna ya kasance mamba a kungiyoyi da dama irin su Ƙungiyar Masana Inshora ta Najeriya, Ƙungiyar Dillalan Inshora da yin Rijista ta Najeriya, Ƙungiyar Inshora ta Afirka ta Yamma, Cibiyar yaki da Haɗɗura ta Najeriya, da Cibiyar Masu Ba da Shawara da Gudanarwa, tare da zama mamba a Asusun Paul Harris na Ƙungiyar Rotary ta Ƙasa da Ƙasa.

Ya shugabanci Ƙungiyar Golf ta Jihar Kano, inda ya rike mukamin shugaban Ƙungiyar Golf ta Kano da kuma Ƙungiyar Rotary ta Bompai.

Ya sami digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Gabashin Tekun Bahar Rum da ke ƙasar Cyprus, sannan ya kammala difloma ta gaba da digiri a fannin kuɗi da gudanarwa daga Jami’ar Loughborough da ke ƙasar Biritaniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here