Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) a ranar Larabar da ta gabata ta lalata kayyakin jabu da wa’adin su suka wuce na sama da Naira miliyan 500 a Abuja.
Da take jawabi yayin atisayen, Darakta Janar na hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin an kuma mikawa hukumar bisa radin kansu.
D-G wanda ya samu wakilcin Mista Francis Ononiwu, daraktan bincike da tabbatar da doka na NAFDAC, ya bayyana cewa ana gudanar da atisayen ne a duk fadin kasar.
Shugaban NAFDAC ya ce an yi lalata da kayayyakin ne domin hana su sake bullo da hanyoyin samar da kayayyaki.