Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa Gowon murnar cika shekaru 89 a duniya

L R Yakubu Gowon and Bola Tinubu
L R Yakubu Gowon and Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya aike da sakon gaisuwa ga tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, murnar cika shekaru 89 a duniya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaban na murna da dattijon da jagororinsa na hangen nesa ya haifar da manyan abubuwa a tarihin Najeriya.

Shugaban ya yabawa Gowon bisa yadda ya kafa tsarin zaman lafiya a Najeriya tare da dawwamammen gado, kamar kafa harsashin tarayyar Najeriya ta hanyar samar da jihohi.

Sauran abubuwan da tsohon shugaban kasar ya dauka sun hada da samar da hadin kai, da karfafa cudanya da fahimtar juna ta hanyar kafa hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC), in ji shugaban.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here