Jami’an tsaro sun samu tallafin ababen hawa a Dawakin Tofa

IMG 20210927 WA0023
IMG 20210927 WA0023

Shugaban karamar hukumar Dawakin tofa Alhaji, Ado Tambai Kwa ya bada gudummuwar motoci da babura na miliyoyin Naira ga jami’an tsaron karamar hukumar domin inganta sha’anin tsaro a yankin.

Ya ce, jami’an tsaro na bukatar ingantattun ababan hawa domin cigaba da kokarin da suke na samar da tsaro ga al’umma, don haka ya zama wajibi ga hukumomi da sauran masu hannu da shuni da su himmatu da tallafawa Jami’an tsaro.

 

Shi ma a nasa jawabin Baturen ƴan sandan yankin Ahamad ya yabawa shugaban karamar hukumar bisa wannan gudummuwa da aka basu, inda ya bukaci jami’an tasaron da suyi amfani da wadannan motoci da babura ta hanyar da ya dace don inganta harkar tsaro a yankin.

A nasa jawabin, Hakimin karamar hukumar Alh Isma’ila Umar Ganduje ya yabawa shugaban karamar hukumar da wannan namijin kokari,inda yace hakan abin koyi ne ga sauran masu rike da madafun iko.

Cikin wadanda suma samu tallafin akwai kungiyat malaman makaranta NUT na karamar hukumar sai kuma injinan wuta da likkafani da sauran kayayyakin karatu ga ‘yan Makaranta don anfanuwar yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here