Gwamnonin Jam’iyyar APC bangaran Arewacin Najeriya sun jaddada matsayarsu kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyar dole ya fito daga Kudu.
Gwamnoin haka kuma sunyi fatakali da zabin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasar Jam’iyyar na masalaha.
Wannan rudanin dai ya kunno kai a yau da ya rage kwana guda zuwa ga taron zaben fidda-gwani da jam’iyar zata gudanar na yan takarar shugaban cin kasa na jam’iyyar ta APC.
Sakomakan rahotanin da ake samu cewa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sanar da cewa Sanata Ahmad Lawan shine dan takarar Jam’iyyar na maslaha.
A wani bangaran Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, ya ce a ganawar da suka yi da shugaba Buhari ranar Litinin, shugaban kasar ya nuna musu goyon bayan sa akan matakin da suka dauka.
Lalong, ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa cewa Buhari ya jaddada musu cewa wajibi ne ayi komai a fili wajen fitar da dan takarar shugaban kasa.
Ya bayyana cewa kuma a halin yanzu Buhari ba shi da dan takarar shugaban kasa, don haka ya bukaci gwamnonin su je su tattauna da Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa (NWC) domin ganin tabbatuwar hakan.
Lalong ya ce a lokacin ganawar tasu, gwamnonin Arewa su 13 sun nemi afuwar Shugaba Buhari, kasancewa sun sanar da shi ma tsayar tasu bayan bullar labarin ta bayan fage.
Sun bayyana masa cewa sun yanke shawarar ce saboda a yi wa kowane bangare adalci a samu zaman lafiya a Najeriya baki daya.
Lalong ya kara da cewa gwamnonin za su yi wani zama a tsakaninsu da yammacin yau Litinin.
Da aka tambaye shi gme da rashin ganin Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a wurin taron, Lalong ya ce Yayaya Bello ba ya cikin wadanda suka amince, hasali ba bai sanya hannu kan takardar bayan taron da gwamnonin suka fitar ba.
Da yake nasa bayanin, Gwamnan Jihar Kaduna, malam Nasir El-Rufai, ya ce Yahaya Bello yana da ’yancin bin raayin kansa.
Mahalarta zaman da gwamnonin suka yi da Buhari sun hada da Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebb; da Lalong da El-Rufai da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum.
Sauran sun hada da Gwamna Abdullahi Sule, Nasarawa; Mohammed Inuwa Yahaya, Gombe; Mai Mala Buni, Yobe; Abubakar Sani Bello, Neja; Abdullahi Umar Ganduje, Kano; da Aminu Bello Masari, Katsina.
Dasu Mohammed Abubakar Badaru, Jigawa da Abdurrahman Abdulrazaq, Kwara. Gwamnan Jihar Kogi kuma mai neman takara, Yahaya Bello bai halarci taron ba.













































