Sarkin Musulmi Ya Ce Musluman Najeriya Su Duba Jinjirin Watan Dhul-Hijjah

0

Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bukaci Musulman kasar da su fara duban jinjirin watan Dhul-Hijjah da yammacin ranar Lahadi Abubakar ya bayar da umurnin ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin bayar da shawarwari kan harkokin addini na masarautar Sokoto.

Dhul-Hijjah ya kasance na 12 kuma na karshe a kalandar Musulunci wanda a cikinsa ne Musulmai ke sauke farali wato aikin Hajji da kuma bikin babban sallah.

“Wannan don sanar da Al’ummar Musulmi ne cewa, Lahadi 18 ga watan Yuni wanda yake daidai da ranar 29 ga watan Dhul-Qadah shine zai zama rana ta karshe da za a nemi jinjirin watan Dhul-Hijjah 1444 AH.

“Don haka ana umurtan Musulmai da su fara neman jinjirin wata a ranar Lahadi sannan su kai rahoton abun da suka gani ga hakimi kauye mafi kusa domin sanar da sarkin Musulmin.” Sanarwar ta kuma roki Allah ya taimaki daukacin al’ummar Musulmi wajen sauke hakokin da ya rataya a wuyansu na addini.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here