Kwankwaso ya goyi bayan Matsayar NDC na baiwa yankin Kudu takarar shugaban kasa ta 2027

Obi and Kwankwaso 750x430

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a ranar Asabar ya goyi bayan maysayar da jam’iyyar NDC na baiwa yankin Kudu tikitin shugaban kasa a shekarar 2027, yana mai cewa matakin ya nuna tsarin rabon mulki da jajircewar jam’iyyar ga adalci.

Kwankwaso ya fadi haka ne a taron kasa na jam’iyyar da aka yi a Abuja yayin da yake jawabi ga wakilai, magoya baya da masu ruwa da tsakin jam’iyyar.

Ya ce, “Ina goyon bayan shawarar kai tikitin shugaban kasa ga Kudu domin yankin ya kammala shekarunsa takwas, wannan na cikin tsarin raba mulki da yarjejeniyar jam’iyyar.”

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da magoya bayan jam’iyyar da su shiga kokarin wayar da kan jama’a kafin zaben shekarar 2027.

“Da fatan a yi rajista yanzu,” in ji shi.

Goyon bayan ya zo ne sa’o’i bayan NDC ta amince da kudurin tikitin shugaban kasa na 2027 ga Kudancin Najeriya na wa’adi daya mai shekaru hudu.

An amince da kudurin ne a taron, bayan wani kuduri da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ogbaru ta Jihar Anambra, Afam Victor Ogene, ya gabatar.

Da yake sanar da shawarar, Shugaban Jam’iyyar na Kada, Moses Cleopas, ya ce tsarin na daga cikin tsarin rabon mulki mai tsari da nufin daidaita bukatun yankuna a cikin hadin gwiwar ‘yan adawa.

Cleopas ya jara da cewa bayan kammala wa’adin Kudu, za a mayar da tikitin shugaban kasa Arewa a 2031.

“Za ta zama lokacin Arewa a 2031,” in ji shi.

Kwamitin Zartarwa na Kasa na jam’iyyar ma ya amince da zaben mambobin Kwamitin Aiki na Kasa a taron.

Ana sa ran tsarin rabon mukaman zai kara karfin tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, da sauran ‘yan takara daga Kudu gabanin zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sake daidaita siyasa gabanin babban zaben 2027, inda ‘yan adawa ke kara karfi wajen gina hadin kai domin fuskantar Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki.

A halin yanzu, Obi da Kwankwaso sun shiga NDC a hukumance a Abuja, inda suka yi kira ga mambobin jam’iyyar da su guje wa rikice-rikice na cikin gida su kuma mayar da hankali kan ci gaban kasa.

Da yake jawabi a taron, Obi ya ce dalilin shigarsu jam’iyyar shi ne bukatar samun dandalin siyasa mai jarfi wanda babu rikicin cikin gida.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here