Tsohon karamin ministan gidaje da raya birane, Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya sayi fom din tsayawa takarar neman kujerar sanata mai wakiltar Kano ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a zaben shekarar mai zuwa 2027.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mataimaki ga tsohon ministan Mansoor Man’ash, ya wallafa a shafin sada zumunta a ranar Laraba, inda yace mai gidan nasa ya shiga neman kujerar.
A cewar sanarwar, dan majalisar wakilai mai wakiltar kan an an hukumomin Gwarzo da Kabo, Hon. Abdullahi Mu’azu Baban Gandu, tare da tsohon Shugaban karamar hukumar Kumbotso, Hon. Hassan Garban Kauye Farawa, ne suka karbi fan din a madadin tsohon ministan.
A yanzu dai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ne sanatan Kano ta Arewa wanda hakan ya sanya ake ganin takarar da ake sa ran a yi a matsayin daya daga cikin yankunan da za ayi siyasa da za a sa ido a kai a jihar gabanin 2027.
Gwarzo, kwararren dan siyasa tsohon mataimakin gwamna, ana sa ran zai yi amfani da kwarewarsa ta siyasa da goyon bayan da yake da shi a kasa wajen yin takara da masana ke hasashen za ta kasance mai zafi a cikin jam’iyyar APC mai mulki.
SolaceBase ta ruwaito cewa sanarwar ta riga ta fara haifar da martani a fagen siyasa, yayin da masu ruwa da tsaki ke nazarin tasirin burin Gwarzo ga tsarin siyasar da ake da shi a Kano ta Arewa.
Zaben shekarar 2027, duk da cewa har yanzu akwai saura, ya fara daukar salo da wuri tare da hadaka da bayyanar niyya da ke nuna tsananin siyasa a Jihar Kano.











































