Shugaba kasa Bola Tinubu ya amince da sauke Saidu Mohammed daga mukamin babban jami’in zartarwa na hukumar kula da harkokin man fetur na tsakiya da kasa (NMDPRA), saboda ra’ayin jama’a.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Shugaban ya kuma amince da nada Rabiu Abdullahi Umar a matsayin sabon babban jami’in zartarwa na NMDPRA. Sai dai nadin na jiran tabbatarwa daga Majalisar Dattawa.
A wata sanarwa da mashawarcin shugaban kasa na musamman a bangaren yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mataki, an dauki wannan mataki bisa dokar masana’antar man fetur ta 2021, an yi shi ne da nufin karfafa ingancin aikin sa ido a bangaren man fetur na tsakiya da na kasa, daidai da Renewed Hope Agenda.
Umar kwararren jami’i ne da ke da kwarewar sama da shekaru 25 a sassan makamashi, masana’antu, da ababen more rayuwa, kuma yana da kyakkyawan tarihi a jagoranci mai dabara, sauya ayyuka, da isar da manyan ayyuka.
Ya kammala karatun Accounting daga Jami’ar Bayero kuma tsohon dalibi ne na makarantar kasuwanci ta Harvard.
Har sai Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabon wanda aka nada babban jami’i mafi girma a NMDPRA zai kula da ayyukan hukumar a matsayin riko.
Shugaba Tinubu ya gode wa babban jami’in zartarwa mai barin gado bisa hidimarsa kuma ya yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.
Shugaban ya kasance mai jajircewa don tabbatar da samun kwararrun shugabanni a manyan cibiyoyin sa ido don ciyar da tsaron makamashi, gyaran bangare, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa gaba.











































