Fadar shugaban kasa ta yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da korar shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.
SolaceBase ta ruwaito cewa wani sako da aka tura ta WhatsApp ya nuna cewa an kori Mahmood tare da maye gurbinsa da Farfesa Bashir Olamilekan.
Sai dai fadar shugaban kasar ta bayyana rahoton a matsayin ‘labari na karya.
A cikin wata sanarwa, O’tega Ogra, babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwar zamani, ya bukaci jama’a su yi watsi da irin wadannan jita-jita.
Ya bayyana cewa duk wata sanarwa a hukumance game da matsayin shugaban INEC za a yi ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya ko wasu majiyoyin gwamnati masu hurumi.










































