Rundunar Sojin Najeriya ta bayar da gidaje ga sojoji 20 da suka jikkata a yayin aiki, a wani bangare na kokarinta na inganta jin dadin ma’aikatanta.
Babban Hafsan Tsaron Kasa, Janar Christopher Musa, ya kaddamar da shirin gidajen sojoji karkashin tsarin Affordable Home Ownership Option for All Soldiers Scheme a Abuja, inda ya mika makullan gidajen ga wadanda suka ci gajiyar shirin.
Musa ya yaba da gudunmawar marigayi Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya fara shirin, tare da jinjinawa sabon Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, kan cigaba da aikin.
Ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi su bayar da filaye don irin wannan shirin, yana mai cewa aikin zai inganta zaman lafiya da cigaban tattalin arziki, tare da rage matsalar gidaje ga sojojin Najeriya.
A cewar Oluyede, shirin zai bai wa sojoji damar mallakar gidaje masu inganci a wuraren da suka zaba bayan ritaya.
Ya ce matakin farko na aikin da aka fara a Abuja zai samar da gidaje ga iyalai 400, yayin da ake ci gaba da shirin a wasu jihohi.