Shida daga cikin ‘yan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya sun janye wa Shekarau

IMG 20260510 WA0257 750x430

‘Yan takara shida da ke neman tikitin Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar APC sun janye domin mara wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, baya, bayan wani taron sulhu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a Masaukin Gwamnan Kano da ke Abuja.

Da yake magana a madadin ‘yan takarar, Usman Bala ya ce sun janye wa Ibrahim Shekarau cikin mutunci domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a cikin jam’iyyar.

Ya bayyana cewa ‘yan takarar sun amince baki daya da shawarar da aka cimma a taron sulhun da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta, kuma sun yi alkawarin bayar da cikakken goyon bayansu domin tabbatar da nasar jam’iyyar APC a jihar.

SolaceBase ta ruwaito cewa ‘yan takar da suka janye su ne Usman Bala, Sha’aban Sharada, Danyaro Yakasai, Abbas Sani Abbas, Abdulfatah Zango da Shehu Isah Direba.

Wannan ci gaban ya biyo bayan makonni na rashin jituwa tsakanin masu ruwa da tsaki kan fitowar Shekarau a matsayin dan takarar yarjejeniya na kujerar Sanata ta Kano ta Tsakiya.

A baya, ‘yan takarar sun ki amincewa da fitowar tsohon gwamnan a matsayin dan takarar yarjejeniya, inda suka jaddada bukatar samun daidaito kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Duk da haka, majiyoyi a taron sun ce tsoma bakin Gwamna Abba ne ya taimaka wajen kwantar da hankali da hada ‘yan takar, wanda ya kai ga yanke shawarar mara wa Shekarau baya gabanin zaben shekarar 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here