Babban taron APC: Buni ya amince da ayyukan da Bello ya yi a matsayin shugaban riko

Mai Mala Buni sabo 1 1
Mai Mala Buni sabo 1 1

Gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin riko da tsare-tsare na jam’iyyar APC, ya amince da matakin da Gwamna Abubakar Bello na Nijar ya dauka a matsayin shugaban riko na kwamitin.

Buni ya tabbatar da ingancin wadannan ayyuka a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake mayar da martani ga rahotannin kafafen yada labarai na cewa ya dakatar da wasu daga cikinsu.

“Ina sanar da duk masu ruwa da tsaki da ‘yan jam’iyyar cewa batun dakatar da wasu ayyuka da CECPC ta fara aiwatarwa a karkashin shugaban riko kuma Gwamnan Neja, Muhammed Bello ba gaskiya ba ne.

“Saboda haka, duk ayyukan da aka yi lokacin da bana nan, suna nan daram kuma suna aiki.

“An shawarci dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ‘ya’yan jam’iyyar da su yi watsi da maganar da ake yadawa ta gabata na yin watsi da ayyukan kwamitin a karkashin jagorancin shugaban,” inji Buni.

Ya ce ya mika ragamar shugabancin kwamitin ga gwamnan Neja kafin ya tafi kasar waje neman lafiya.

“Saboda haka, duk wani mataki da matakan da kwamitin ya dauka a matsayinsa na shugaban riko na ci gaba da yin tasiri,” inji Buni wanda shi ne Gwamnan Yobe.

Ya bukaci goyon baya da fahimtar ‘ya’yan jam’iyyar don ciyar da ita gaba zuwa babban taron kasa da aka shirya yi a ranar 26 ga Maris.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here