Gwamna Aliyu na Sokoto ya raba kyautar Naira 450,000 ga kowane Alhajin jihar

Ahmed Aliyu 750x430

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayar da gudunmawar Riyal 1,000 na kasar Saudiyya, kwatankwacin Naira 450,000 ga kowane mahajjatan jihar a matsayin kyautar Sallah.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai wa Alhazan jihar ta Sokoto da ke Mina, inda ya taya su murnar kammala aikin Hajjin bana.

Aliyu ya ce, an yi hakan ne da nufin tallafa wa alhazai da kudade yayin da suke shirin dawowa gida Najeriya.

Haka kuma, ya bayyana jin dadinsa da yadda mahajjatan jihar suka gudanar da aikin hajjin bana, inda ya ce, babu wanda aka samu ya karya dokokin Saudiyya a lokacin da suke kasa mai tsarki.

Gwamna Aliyu ya kuma yaba wa Amirul Hajj na jiha Alhaji Ummarun Kwabo, bisa namijin kokarin da ya ke yi na ganin an samu nasarar aikin hajjin bana.

Daga karshe, ya yaba wa jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jihar Sokoto bisa jajircewar da suka yi wajen gudanar da aikin hajji cikin nasara.

Ya bukaci mahajjatan da su kara himma wajen addu’o’i ga Najeriya, musamman neman taimakon Allah wajen magance dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta, tare da mai da hankali kan rashin tsaro.

Gwamnan ya kuma yi amfani da ziyarar wajen jajanta wa alhazan kananan hukumomin Gudu da Shagari bisa rasuwar Hajiya Hadiza da Bala Jangebe, wadanda suka rasu a yayin gudanar da aikin hajjin, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

A nasa jawabin tun da farko, Amirul Hajj na jihar, Alhaji Ummarun Kwabo, ya gode wa gwamnan bisa tallafin da ya raba, wanda ya ce, ya taimaka matuka wajen samun nasarar ayyukan Hajjin bana.

Ya yi nuni da cewa, dukkanin kwamitocin da aka kafa domin gudanar da aikin hajjin sun yi aiki tukuru domin ganin an gudanar da aikin hajji cikin nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here