Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, ta bayyana cewa wani waje na wurin hakar ma’adinai ya ruguje a kauyen Galkogo da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, inda ya kashe mutum daya tare da jikkatar wadanda suka makale sama da mutum 30 a jihar.
“An tabbatar da mutuwar mutum daya, an ceto mutane shida da munanan raunuka yayin da sama da mutane 30 ke ci gaba da kulawa,” in ji hukumar.
Karin labari: “Zan riƙa samun sama da dala miliyan dubu 30 nan da ƙarshen 2024” – Ɗangote
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Abdullahi Baba-Arah, ne ya bayyana haka a Minna a ranar Talata cewa lamarin ya faru ne a ranar 3 ga watan Yuni 2024.
Ya ce hukumar ta samu rahoton rugujewar wani wurin hakar ma’adinai a kauyen Galkogo na Shiroro.
Baba-Arah ya ce dalilin rugujewar wurin hakar ma’adinan ya faru ne sakamakon ruwan sama da aka yi ta yi.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Kungiyoyin Kwadago sun dakatar da yajin aiki na mako daya
Sai dai ya nuna damuwarsa kan yadda masu aikin ceton suka gudu daga wurin domin ceto wurin da lamarin ya faru.
Ya kuma kara da cewa har yanzu hukumar ba ta samu cikakken bayani kan ayyukan ceto ba sakamakon rashin tsaro da ake fama da shi a yankin.
Babban daraktan ya kuma ce hukumar ta samu rahoton hare-haren ‘yan bindiga da ake ci gaba da kai wa a kananan hukumomin Shiroro da Mashegu na jihar.
Karin labari: Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya damu kan zargin karin girman wasu jami’ai ba bisa ka’ida ba
Ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Adogo Malam a ranar 2 ga watan Yuni inda suka yi garkuwa da mutane shida.
Ya kuma ce ‘yan bindigar da ake zargin sun yi garkuwa da mutane sama da 20 tare da sace shanu da dama a Tunga Kawo, wata unguwa da ke makwabtaka da Erena, kamar yadda NAN ta tabbatar.