Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana matukar damuwarta kan rahotannin karbar kudade da kuma rashin da’a da ke tattare da karin girma da ake yi wa masu neman mukamin mataimakin Sufeton ‘yan sanda.
SolaceBase ta bayyana cewa Rundunar ta ce irin wannan ɗabi’a na lalata ainihin ƙimar cibiyar kuma ba za a amince da hakan ba.
Karin labari: Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta gayyaci ma’aikata kan yajin aikin mafi karancin albashi
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Talata, ta ce babban sufeton ‘yan sandan kasar, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya yi kakkausar suka ga duk wani nau’i na cin hanci da rashawa da ake yi a harkar karin girma.
Sannan ya bukaci dukkan jami’an da su kai rahoton duk wani abu da ya faru da su cikin gaggawa. Kai tsaye zuwa ga IGP ta hanyar wayar da aka ware a 09077120194 ko kuma zuwa ga Jami’in Hulda da Jama’a (FPRO) a 08037168147.
Karin labari: Ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya ta bi sahun yajin aikin ƙwadago
“A bisa wadannan zarge-zarge, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sake tabbatar da aniyar ta na tabbatar da gaskiya da rikon amana a dukkan matakan kara girma.
“Duk wani jami’in da aka samu yana aikata cin hanci da rashawa don amfanin kansa, zai fuskanci tsauraran matakan ladabtarwa,” in ji sanarwar.
“An yi kira ga dukkan jami’an da su kiyaye ka’idojin da’a tare da yin aiki tare don tabbatar da gaskiya da amincin rundunar ‘yan sanda.