Barau ya bukaci hukumomin tsaro su dauki mataki kan ’yan bindiga da ke barazana al’ummomin Kano

WhatsApp Image 2025 09 18 at 18.50.08 750x430

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bukaci hukumomin tsaro da su farauto ’yan bindiga da ke addabar wasu kauyuka a ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono na jihar Kano.

A martaninsa game da harin ’yan bindiga a kauyen Ƴankamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a daren Asabar, Sanata Barau ya roki hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi tare da kai farmaki kan miyagun ɗaiɗaikun mutane da ke fitowa daga jihohin makwabta.

Sanata Barau, cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, ya ce dole a kawo ƙarshen shiga yankunan biyu da miyagun ke yi.

Ya ce ya samu rahoton kisan wata mata da kuma sace mutane uku da ’yan bindigar suka yi a kauyen Ƴankamaye a tsanyawa, inda maharan daga jihohin makwabta suka kai farmaki yayin da jama’a suka kwanta barci.

Ya ce wannan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan makamancin harin da aka kai a kauyen Biresawa, shima a cikin Tsanyawa, don haka dole hukumomin tsaro da ke yawan fuskantar maharan a yankin su ƙara kuzari wajen ceto waɗanda aka sace da kuma magance miyagun.

Ya ƙara da cewa ba za a bar waɗannan ’yan bindigar da ke gudu daga jihohin makwabta bayan farmakin sojoji su tarwatsa zaman lafiya a al’ummomin jihar ba.

A cewtsa, shiga yankin dole ne don tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar ya fi komai muhimmanci, babu wani abin da za a yi watsi da shi wajen tabbatar da hakan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here