Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Litinin ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane tara a kauyen Rugar Kusa da ke karamar hukumar Musawa ta jihar.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma tabbatar da cewa mutum 16 sun samu raunuka daban-daban a lokacin da maharan suka far wa musulmin da ke bikin Mauludi a ranar Lahadi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ya fitar.