Zamu Gabatar Da Alasan Ado Doguwa A Gaban Kotu – Yan Sanda

blog post708
blog post708
Rundunar yan sanda ta jihar Kano, tace zata gabatar da dan majalisar Doguwa da Tudun Wada, Alasan Ado Doguwa, a gaban kotu nan gaba kadan, domin tuhumarsa bisa zarge-zarge da ake yi masa na aikata ta’addanci a lokacin zaɓe.
Kakakin hukumar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a yau, inda yace tun a ranar 27 ga watan Fabrairu suka aikawa Alasan da sakon gayyata amma yaƙi amsa gayyatar, saboda haka a ranar 28 ga watan Fabrairu suka cafke shi a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano.
Ana zargin Alasan da farwa wasu mutane magoya bayan jam’iyyar NNPP hari, tare da ƙone ofishin na NNPP, lamarin da yayi sanadin mutuwar mutane da jikkatar wasu, a lokacin bayyana sakamakon zaɓen shekarar 2023 da aka gudanar a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here