Majalisa Ta 10: Ba Na Sha’awar Neman Shugabancin Majalisa – Ahmad Lawan 

Ahmed Lawan
Ahmed Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya karyata jita-jitan da ake yadawa cewa yana son tsayawa takarar shugabancin majalisar. Lawan ya fadi haka ne ga ‘yan jaridu bayan kammala ganawarsu da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis 1 ga watan Mayu.

Ganawar ta samu halartar maitaimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, cewar Premium Times.

Ya bayyana cewa bai taba nuna sha’awar neman takarar ba saboda ba ya bukata, ya ce bayan shafe shekaru 24 a majalisar, lokaci ya yi da ya kamata ya taimaka wa sabbin ‘yan majalisu da aka zaba.

“Ba na bukatar zama shugaban majalisar, na ba da gudumawar da zan bayar, kuma ina murnar irin gudumawar da muka bayar, ban taba nuna sha’awan neman takarar ba.”

Ahmad Lawan an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai a shekarar 1999 kafin ya koma majalisar dattawa.

Ya kara da cewa, akwai wasu matsaloli da ya kamata a kawo karshensu, inda ya ce zaben shugabancin majalisar bai kamata son rai ya shiga ciki ba, sai dai duba ci gaban kasa da kuma majalisar.

“Abin da ya kamata a duba shi ne ci gaban kasa da kuma majalisar, don haka dole a saka kowa da kowa a lamarin. “Muna da tabbacin samun nasara, yadda Shugaban kasa a matsayinsa na tsohon sanata, da kuma mataimakinsa shi ma ya kasance a majalisar, wannan shi ne abin da kullum muke addu’an samu.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here