Akalla ‘yan kasuwa 18 ne suka rasu a hatsarin mota kan hanyar su ta kai shanu zuwa Legas daga Sokoto a yammacin ranar Litinin.
A cewar rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta ce an kai fasinjoji 42 da suka samu raunuka a hatsarin zuwa asibiti a yankin Gwandu da ke jihar.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa shanu 16 sun rasu a hatsarin.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da direban wata babbar mota ɗauke da fasinjoji da shanu daga yankin Illela na jihar Sokoto ya kauce hanya a mahaɗar Malisa, inda nan take motar ta faɗi kasa.
Ya ce hakan ne ya janyo rasuwar fasinjoji 18 yayin da 42 kuma suka samu raunuka daban-daban.
SP Nafiu Abubakar ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kebbi, Ahmed Magaji Kontagora, ya tura jami’an ‘yan sanda zuwa wajen domin ɗaukar waɗanda suka jikkata zuwa asibiti don yi musu magani.
Kwamishinan ‘yan sandan ya miƙa ta’azziya zuwa ga iyalan waɗanda suka rasu, inda kuma ya buƙaci kungiyoyin NURTW da NARTO da sauran masu amfani da hanya da su rika lura da abubuwan rage gudu da kaucewa ɗaukar kaya fiye da ƙima da kuma mayar da hankali yayin tuki.












































