Kotun Daukaka Kara dake Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke ranakun da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar na zaben 2027.
A cikin wani hukunci na bai-daya da kwamitin alkali 3 suka yanke a ranar Alhamis, Kotun Daukaka Karar ta amince da daukaka karar da INEC ta yi tare da warware hukuncin kotunfarko na ranar 20 ga Mayu.
Kotun Daukaka Kara ta ce kotun farko ta gaza bin hukunce-hukuncen shari’a na baya da suka zama dole a bi. Ta kuma yanke hukuncin cewa Sabon Teburin Zaben 2027 na INEC doka ce ta biyu karkashin Dokar Zabe ta 2026 kuma tana da karfi irin na dokar kanta.
A cewar kotun, INEC ta yi aiki ne bisa ikon da doka ta ba ta, ta kara da cewa duk ranakun da aka sanya a cikin sabon jadawalin na cikin tanadin Dokar Zabe.
INEC ta shigar da sanarwar daukaka karar a ranar 25 ga Mayu, inda ta kawo dalilai 9, tana rokon Kotun Daukaka Kara da ta soke hukuncin kotun farko.
Hukumar ta yi gardamar cewa kotun farko ta gaza yanke hukunci a kan batun ikon sauraron shari’a da ta tayar, sannan kuma karar da Jam’iyyar Matasa ta Youth Party ta shigar kara ce ta banza da ba ta da wani tushe.
Haka kuma, INEC ta ce rashin yanke hukunci a kan wadannan batutuwa da kotun ta yi ya hana ta samun shari’a ta adalci.












































