A kalla Mutane 45 ne suka mutu yayin da wasu 27 suka jikkata sakamakon sabon rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a yankin Lafia, Obi da Awe dake jihar Nasarawa.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi arangamar ne daga safiyar ranar Juma’a har zuwa daren Lahadi.
Wata majiya ta ce akalla manoma 5,000 daga cikin al’ummomi 12 ne suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren da aka kai a kananan hukumomin uku.
Majiyoyi da hukumomi sun ce wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka a halin yanzu suna samun kulawa a asibitocin kananan hukumomin Obi, Lafia da Awe.
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da faruwar lamarin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Ramhan Nansel, ya ce sun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai wa wani Umaru Idrisu na kauyen Gidan Washi da ke karamar hukumar Obi hari tare da kashe shi.
Ya ce bayan karbar korafin kwamishinan ‘yan sandan, Mista Adesina Soyemi, ya umarci jami’in ‘yan sanda na Dibisional (DPO) na karamar hukumar Obi da ya garzaya wurin da aka tsinto gawar sannan aka garzaya da ita asibiti domin yin bincike kafin a mika ta ga iyalai don binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.













































