Buhari yaki sanya hannu kan sabuwar dokar zabe

6816BA0C 434E 4220 9E4A 162B96A92C79
6816BA0C 434E 4220 9E4A 162B96A92C79

Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya karanta wasikar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kin amincewa da amincewa da gyaran dokar zabe a zaman majalisar na yau Talata.

Wasikar ta ce Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya samu cikakken bayani daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da abin ya shafa, sannan na yi bitar kudirin a tsanake bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a Tarayyar Najeriya a halin yanzu.

“Sakamakon bitar, mai girma shugaban majalisar wakilai na iya lura da cewa, gudanar da zabukan fitar da ‘yan takarar jam’iyya ta hanyar zaben fidda gwani kai tsaye kamar yadda dokar zabe ta 2021 ta tanada yana da mummunar illa, shari’a, kudi, tattalin arziki da kuma illar tsaro da ba za a iya shawo kanta ba a halin yanzu idan aka yi la’akari da irin abubuwan da al’ummarmu ke da shi.” A cewar shugaba Buhari ta cikin wasikar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here