Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai a fadar shugaban kasa dake Abuja a yau Talata.
Gwamna El-Rufai ya samu rakiyar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan.
Rahotonni sun bayyana cewa sun yi wata ganawar sirri, wanda kawo yanzu ba’a san mai suka tattauna ba.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jihar Kaduna ke fama da karuwar hare-haren ‘yan bindiga tare da satar mutane a ciki da wajen jihar.













































