Yanzu-yanzu: Ɗan wasa Dambele ya lashe kyautar Gwarzon ɗan wasan Duniya ta Ballon d’Or

images voltaxMediaLibrary mmsport si 01k5skbm25knahb827xe 750x430

Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint-Germain Ousmane Dembélé ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Duniya ta FIFA Ballon d’Or

Hakan na zuwa a lokacin da aka bayyana sunan sa a bikin bayar da kyautuka na yan wasan da suka nuna hazaka a kakar wasanni ta shekarar 2024/2025 da ta gabata.

Taron ya gudana dai a dakin taro na Théâtre du Châtelet dake birnin Pari na ƙasar France.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta ƙasar France wato PSG ta lashe dukkan gasar da ake bugawa a kasar kuma ta Lashe kofin zakarun Turai ta Champion League da taimakon ɗan wasan Dambele.

Yayin bayar da kyautukan dai ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona Lamine Yamal ne ya yi na biyu kuma ya lashe kyautar matashin dan wasan da ya fi kowa hazaƙa a gasar.

Danbele dai ya zura ƙwallaye 35 da bayar da taimako 16 tare da lashe manyan gasar wasanni da ƙungiyar ta halarta.

Mai tsaron ragar ƙungiyar ta PSG da ya sauya sheka zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City Dannaruma ne ya lashe kyautar mai tsaron ragar da ya fi kowa kokari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here