“Na sulhunta da Wike” Fubara ya yi bayani bayan ganawa da Tinubu

President Tinubu received Fubara at the State House on Monday September 22 2025

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa siyasar jihar ta daidaita bayan sulhu tsakaninsa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Fubara ya yi wannan bayani ne a fadar shugaban ƙasa bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a Abuja ranar Litinin, 22 ga Satumba, 2025.

Ya ce rikicin siyasar Rivers da ya jawo dakatar da shi daga mukaminsa na tsawon watanni shida ya ƙare, kuma yanzu yana aiki tare da Wike.

Fubara ya gode wa Tinubu bisa rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar, yana mai cewa ziyarar tasa ta nuna godiya ce ga shugaban ƙasa.

Labari mai alaƙa: Tinubu ya ɗaga dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Idan za a iya tunawa cewa, an dakatar da Fubara da mataimakinsa da kuma ’yan majalisar dokoki na jihar a ranar 18 ga Maris, 2025, sakamakon rikicin siyasa.

Sai dai daga baya Tinubu ya jagoranci sulhu tsakaninsa da manyan ’yan siyasa na jihar, ciki har da Wike.

A ranar 17 ga Satumba, 2025, shugaban ƙasa ya sanar da kawo ƙarshen dokar ta-baci a jihar, abin da ya baiwa Fubara damar komawa ofis a ranar 19 ga Satumba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here