Hukumar kwastam ta tsawaita aikin tan tance  jiragen sama masu zaman kansu

Private Jet

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta tsawaita tantance dawo da jiragen sama masu zaman kansu da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba da wata daya, daga ranar 14 ga Oktoba zuwa 14 ga watan Nuwamba.

Abdullahi Maiwada, kakakin hukumar NCS ne ya sanar da tsawaita wa’adin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.

A cewar Maiwada, wannan tsawaita ta samar da ƙarin  ga masu sarrafa jiragen sama masu zaman kansu don bin ka’idojin da suka dace da kuma cika wajibcinsu.

Maiwada ya jaddada kudirin hukumar ta NCS na tabbatar da duk jiragen da ake shigowa da su ba bisa ka’ida ba sun cika sharuddan doka, da inganta gaskiya da rikon amana a bangaren sufurin jiragen sama.

Ya kuma karfafa gwiwar masu sarrafa jiragen da su yi amfani da tsawaita lokacin don kaucewa takunkumin da ya biyo bayan cikar wa’adin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here