CSSN ta karrama shugabar WOFAN, Dr. Salamatu Garba, Kan Gudummawarta ga cigaban al`umma

IMG 9019

Kungiyar Kimiyyar Noma ta Najeriya (CSSN) ta karrama Hajiya Salamatu Garba, Daraktar gidauniyar WOFAN, saboda irin gudummawar da ta bayar wajen karfafa mata da matasa, musamman a bangaren noma.

Shugaban CSSN, Farfesa M.I. Uguru, ya yaba wa Dr. Garba saboda shekarun da ta shafe tana hidima ga cigaban al’umma.

A yayin taron kasa na 9 na CSSN a Jami’ar Bayero, Kano, tsohon dan majalisar wakilai Munir Babba Danagundi ya bayyana ta a matsayin gagarumar jigo a bangaren noma, yana mai nuna yadda take amfani da dukiyoyin da aka bata wajen cigaban al’umma.

A na ta bangaren, Dr. Garba ta nuna godiya, inda ta ce hakan ya tuna ma ta tafiyarta tun daga lokacin da ta kafa WOFAN a shekarar 1993.

A karkashin jagorancinta, WOFAN ta taimaka wajen karfafa dubban mata da matasa na karkara, ta hanyar mayar da noma kasuwanci mai riba.

Haka kuma, kungiyarta ta bada gudummawa wajen gina makarantu, masallatai, da kuma kayan tsafta a al’ummomi.

Dr. Garba ta samu lambar yabo da dama, ciki har da lambar yabo ta Value4Her saboda kafa kasuwancin noma sama da 5,000 da mata da matasa suka jagoranta a Najeriya.

Tana da manyan digiri na biyu daga Jami’ar Ahmadu Bello da Jami’ar Wolverhampton, kuma aikinta ya bata matsayin Jakadiyar Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UN).

Taron ya samu yabo daga mahalarta da dama, inda suka jinjina wa Dr. Garba bisa jajircewarta wajen karfafa al’umma da inganta noma mai dorewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here