Yanzu Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da Adeleke a matsayin gwamnan Osun.

A yau Talata ne kotun koli ta tabbatar da Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin sahihi kuma zababben gwamnan jihar Osun.

Mai shari’a Emmanuel Agim, wanda ya karanta hukuncin a ranar Talata ya tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da nasarar zaben Ademola Adeleke.

Kwamitin alkalai mai mutune biyar na kotun koli ya ce kotun daukaka kara da ta tabbatar da Adeleke a matsayin gwamna daidai ne.

Idan dai za a iya tunawa Oyetola da jam’iyyar sa ta APC sun garzaya kotun koli ne kan wata kara mai lamba SC/CV/510/2023, inda suka roki kotun da ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta Abuja ta yanke wanda ya karyata hukuncin da kotun baya da ta yanke.

Idan za a iya tunawa kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar Osun, wadda ta mayar da Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here