An dage zaman majalisar wakilai har zuwa ranar 16 ga Mayu, 2023.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar Dokta Yahaya Danzaria ya fitar a ranar Talata 9 ga watan Mayu, 2023, a Abuja.
Ya ce ranar da aka dage zaman tun da farko na ranar 9 ga watan Mayu, ba zai yiwu ba saboda hakan ba zai baiwa ‘yan majalisa dama ba a shirin kaddamar da majalisar ta 10 da ke gudana.
“Da haka ake sanar da daukacin ‘yan majalisar wakilai da sauran jama’a cewa majalisar wakilai ba za ta dawo zamanta ba a ranar Talata 9 ga watan Mayu 2023 kamar yadda aka tsara zaman a baya. Izuwa yanzu an dage zaman zuwa Talata 16 ga Mayu 2023.
“Wannan canjin an yi niyya ne don baiwa Membobi damar shiga cikin shirin kaddamar da Majalisar Dokoki ta Kasa ta 10 da ke gudana. Majalisa na bada hakuri ga wanda sauyin bai yiwa dadi ba, ”in ji sanarwar.










































