Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari garin Tsafe hedikwatar karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara inda suka kashe dan kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar DIG Mamman Tsafe da wasu mutane uku.
Harin dai ya faru ne a daren Lahadi a lokacin da ‘yan bindigan sanye da kakin soji suka kai farmaki a unguwar Shiyar Namada da ke garin.
Mutanen da ba a san su wane ba, ba jami’an soji ba ne, domin wasu mazauna garin da tun da farko suka gan su, sun dauke su a matsayin jami’an tsaro da ke sintiri akai-akai.
An tattaro cewa dan kwamishinan da ke zaune a kofar gidansu a lokacin buda baki tare da wasu ‘yan bindigar sun kasa gudu yayin da ‘yan bindigan suka bude musu wuta inda suka kashe su nan take.
Wata majiya a safiyar ranar Litinin da ta yi karin haske kan harin ta ce a lokacin da nake magana da ku a safiyar yau ina gidan Waziri inda ake shirye-shiryen jana’izar su.”
Sai dai kuma an tattaro cewa harin na iya zama harin ramuwar gayya, yayin da jami’an ‘yan banga da aka fi sani da Yan Sakai suka fille kan wani dan bindiga da aka gan shi a bakin garin a ranar Juma’ar da ta gabata.
Har zuwa lokacin gabatar da rahoton, rundunar ‘yan sandan jihar ko kuma gwamnatin jihar har yanzu ba su mayar da martani kan lamarin ba.










































