Rundunar Sojojin Najeriya ta karyata wata sanarwa ta bogi da ke yawo a shafukan sada zumunta da sauran shafukan yanar gizo, wanda ke gayyatar mutane domin neman shiga aikin Short Service Combatant Commission (SSC) Course 50/2027.
Mataimakiyar Daraktar hulda da jama’a ta rundunar, Kanar Appolonia Anele ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin. Ta bayyana sanarwar a matsayin ta karya, zamba, kuma mara izini.
Anele ta gargadi jama’a, musamman wadanda ke son nema, da su yi watsi da sanarwar tare da gujewa biyan kudi ga mutane ko shafuka da ke da’awar suna daukar ma’aikata a madadin Sojoji.
Ta sake jaddada cewa dukkan ayyukan daukar ma’aikata da nadin mukamai na Sojojin Najeriya kyauta ne, ana yin su cikin gaskiya kuma bisa cancanta kawai.
A cewarta, ana fitar da sanarwar daukar ma’aikata na hukuma kawai ta hanyar manyan jaridun kasar nan, da shafukan sada zumunta na Rundunar Sojojin Najeriya ingantattu da sauran kafafen sadarwa na hukuma da aka amince da su.
Ta jaddada cewa ba a siyar da wani fom din nema, kuma ba a ba kowa ko wani wakili izinin taimakawa wajen daukar ma’aikata ko neman kudi a kowane mataki na aikin ba.
Anele ta ce an sanar da hukumomin tsaro domin gano, kama da gurfanar da wadanda ke shirya wannan sanarwar ta jabu.
Ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana kirkira, yadawa ko amfani da sanarwar jabu don zambatar ‘yan Najeriya zai fuskanci hukuncin doka.
Mai magana da yawun Sojoji ta bukaci ‘yan Najeriya su tabbatar da kowanne bayani na daukar ma’aikata ta hanyar tashoshi na hukuma na Rundunar Sojojin Najeriya, kuma su kai rahoto kan duk wani shakku na daukar ma’aikata ga sansanin soji mafi kusa ko hukumar tsaro. (NAN)













































