Mukaddashin Daraktan Yada Labarai da Kididdiga na Kotu daukaka kara ta Shari’a ta Jihar Kano, Muzambilu Ado ya shigar da karar Hukumar Shari’a ta Jihar (JSC) yana kalubalantar tilasta masa yin ritaya da aka yi saboda zargin tafka magudi a bayanan karatunsa.
An shigar da karar a gaban Kotun Ma’aikata ta Kasa (NIC), ta kuma ambaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan Shari’a na jihar a matsayin wadanda ake kara.
Ado yana neman a biya shi diyyar naira miliyan 100, inda yake zargin cewa umurnin da hukumar JSC ta bayar na tilasta masa yin ritaya ya bata masa suna, sannan ya ruguza kyakkyawan aikin da ya gina tsawon shekaru.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa, hukumar JSC ta sanar da tilasta wa Ado yin ritaya cikin gaggawa a wata sanarwa da ta fitar ranar 6 ga watan Yuli.
Hukumar ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne biyo bayan binciken da Kwamitin Daukar Ma’aikata na hukumar ya gudanar, wanda ta yi zargin ya gano kura-kurai masu yawa a takardun karatun Ado, da suka hada da canza bayanan karatu da kuma shiga Makarantar Horar da Lauyoyi ta Kasa ba tare da amincewar hukumar ba.
A cikin bayanin da’awarsa, Ado ya musanta dukkan zargin tafka magudi da kuma sauya bayanai a takardun karatunsa.
Ya jaddada cewa an dauke shi aiki a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ne a shekarar 2006 da takardar shaidar Diploma a fannin Gudanarwa daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, kuma bai taba gabatar da takardar shaidar HND ba lokacin da aka dauke shi aiki ko kuma lokacin ayyukan tantancewa a baya.
A cewarsa, zargin da hukumar ke yi masa na cewa ya yi jabu tare da sauya maki a takardar HND ba shi da tushe balle makama.
Game da karatunsa na aikin lauya kuwa, Ado ya bayyana cewa ya yi rajista a Kwalejin Jami’ar Imperial da ke Sudan, inda ya sami digirinsa na farko a fannin Shari’a (LLB) a shekarar 2022.
Ya kara da cewa makarantar ta tabbatar wa hukumar JSC ta Kano cewa an ba shi gurbin karatu na LLB a ka’idance kuma ya kammala dukkan kwasa-kwasan da aka tsara masa cikin nasara.
A cewarsa, jami’ar ta kuma yi bayanin cewa da fari ya yi karatun Shari’a da Shari’ar Musulunci da ta Kasa ne a Jami’ar Alnahda ta Kasa da Kasa da ke Jamhuriyar Nijar, kafin ya koma Jami’ar Imperial bayan da aka yi zargin Jami’ar Alnahda ta gaza tura sunansa don shirin neman gurbin shiga makarantar lauya na ‘Bar Part I’ saboda rashin samun amincewa da ya kamata.
Ado ya kuma musanta ikirarin hukumar JSC na cewa ta gudanar da binciken ne sakamakon takardar korafi da wani mai suna Sani Manzo ya shigar, inda ya bayyana sunan a matsayin na bogi.













































