Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya ta tsare jami’anta hudu bisa zargin karbar na-goro da karfin tsiya har naira 53,000 daga hannun Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Sauran Laifuka Masu Alaka (ICPC) Dr Musa Aliyu (SAN), yayin da suka tsayar da shi ba bisa ka’ida ba don binciken a Abuja.
Kwamishinan ‘yan sandan Babban Birnin Tarayyar, Ahmed Sanusi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Abuja, inda ya bayyana jami’an a matsayin “barayi” wadanda ba su dace su sanya kakin ‘yan sanda ba.
A cewarsa, jami’an sun kafa shingen binciken ababen hawa ba tare da izini ba a yankin Banex da ke Wuse bayan sun bar guraren aikinsu na ka’ida, inda suka karbi kudin a hannun shugaban ICPC ba tare da sanin ko shi wane ne ba.
Ya ce an tilasta wa shugaban na ICPC cire naira 53,000 ta hannun mai sana’ar PoS, har ma ya biya kudin cirewa kafin jami’an su raba kudin a tsakaninsu.
“Ina mai tabbatar muku cewa muna da ‘yan sanda kusan hudu a tsare a yanzu haka wadanda suka yi nasarar karbar kudi a hannun wani babban mutum, ba tare da sanin shi din babban jami’i ne a cikin al’umma. A bayyane yake, Shugaban ICPC suka yi wa wannan abu.
Sun karbi N53,000 a hannunsa, bayan sun kai shi wurin POS, ya cire kudin, ya biya kudin cirewa, sannan suka raba kudin a tsakaninsu,” in ji shi.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce bincike ya gano cewa jami’an sun bar guraren aikinsu da aka tsara musu, inda suka kafa kungiyar barayi tare da kafa shingen bincike na haram domin karbar kudi a hannun direbobi.
Sanusi ya ce rundunar ta ayyana neman jami’an kafin ta kama shugaban kungiyar tasu, wanda amsa laifinsa ya kai ga kama sauran membobin kungiyar.
Kwamishinan ya sake jaddada cewa Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda ya haramta binciken wayoyin salula na ‘yan kasa ba gaira ba dalili ta hanyar jami’ai masu sintiri.
Ya bukaci al’umma da su hanzarta bayar da rahoton duk wani lamari na karbar kudi da sauran ayyukan ba daidai ba da jami’an ‘yan sanda ke yi, tare da ba da tabbacin cewa za a gano masu laifin kuma a hukunta su.
“Za mu ci gaba da amfani da umarnin IG, wasu daga cikinsu suna yin hakan ne saboda suna da tunanin aikata laifi. Suna so su gudanar da irin wadannan ayyukan. Idan muka kama su, za su fuskanci matakan ladabtarwa kuma za a sa su dandana sakamakon abin da suka shuka,” in ji Sanusi.













































