Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ba da umarnin rushe dukkan kwamitocin wicin-gadi na majalisar kasa nan take, wanda hakan ya kawo karshen ayyukansu tun daga 28 ga Agusta 2026.
Umarnin ya fito ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Majalisar, Sidi Ibrahim, ya fitar a ranar Asabar kuma aka tura wa shugabanni da mambobin kwamitocin da abin ya shafa.
Sakatariyar ya ce Shugaban Majalisar ya ba da umarnin rushe kwamitocin ne bayan karewar wa’adin da aka ba su da farko na kammala ayyukansu da mika rahotanni.
“Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, Ph.D., GCON, ya umarce ni da in sanar da dukkan ‘yan Majalisa masu girma cewa dukkan Kwamitocin wicin-gadi na Majalisar an rushe daga yanzu” in ji umarnin.
Ibrahim ya bayyana cewa majalisar ta roki kwamitocin da su kammala ayyukansu a cikin wa’adin da aka ba su.
Ya ce kwamitocin wicin-gadi guda 2 ne kawai suka nemi karin lokaci don kammala aikinsu kuma aka ba su makonni 2 na kari.
A cewar sa, wannan karin lokacin ya kare, saboda haka babu wani dalili da zai sa kwamitocin su ci gaba da aiki.
“Don gujewa kokwanto, muna tuna wa ‘yan Majalisa masu girma cewa kwamitocin wicin-gadi kwamitoci ne da majalisa ta kafa don wata manufa ta musamman da takamaiman lokaci,” in ji shi.
“Ba a yi niyyar su ci gaba da wanzuwa har abada ba bayan manufar da lokacin da aka kafa su.”
Sakataren ya bayyana Doka ta 18, Sashe na 11 sakin layi na 5 na Dokokin Tsarin Majalisar, wanda ya tanadi iyaka game da lokacin mika rahotanni na kwamitoci.
“Bisa ga Doka ta 18, Sashe na 11, sakin layi na 5, na Dokokin Tsarin Majalisar Wakilai, wanda ya tanadi ‘iyaka game da lokacin mika rahotanni’, dole ne kwamitoci su mika rahotanninsu a cikin lokacin da aka ba su,” in ji Ibrahim.
Ya kara da cewa kwamitocin sun zarce lokacin da aka ba su, don haka ci gaba da wanzuwarsu bazai yiwuwa ba.
Sanarwar ta kara da cewa an fara aiki da rushewar ne daga Juma’a, 28 ga Agusta 2026, kuma an ba da umarnin a dakatar da duk ayyukan da ake yi da sunan kwamitocin da aka rushe.
“Saboda haka, tun daga Juma’a 28 ga Agusta 2026, dukkan kwamitocin wicin-gadi na majalisar an rushe su, kuma duk ayyukan da ake gudanarwa da sunan irin wadannan kwamitoci za su tsaya nan take,” in ji sakatariyar.
An kuma umarci shugabannin kwamitocin da abin ya shafa da su mika duk rahotannin da suka rage, takardun aiki da sauran bayanan da suka shafi ayyukansu zuwa ofishin Sakataren Majalisar domin adana su.
“Ana umartar shugabannin kwamitocin da abin ya shafa da su aika duk rahotannin da suka rage, takardun aiki, bayanai da sauran kayan da suka shafi ayyukansu zuwa ofishin Sakataren Majalisar Wakilai domin adana su,” in ji Ibrahim.













































