‘Yan bindiga sun yi garkuwa da malami da wasu mutane 4 a Yobe – ‘Yan sanda

Gunmen
Gunmen

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe a ranar Larabar ta tabbatar da sace Babagana Kachalla, mataimakin shugaban makarantar Central Primary Buni Yadi da wasu mutane 4 da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyen Madiya da ke karamar hukumar Gujba a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu.

Abdulkarim ya lissafa sauran wadanda aka sace sun hada da Abubakar Barma, Haruna Barma, Modu Bukar da Hajiya Gana.

Ya ce lamarin wanda ya faru da misalin karfe 8:20 na safiyar ranar Talata, wani Mala Boyema ne ya kai rahotonsa ofishin ‘yan sanda na yankin da misalin karfe 10:37 na safe.

Kakakin ya ce, Boyema ya yi sa’a ya tsallake rijiya da baya daga garkuwar da wasu mahara dauke da muggan makamai suka yi a lokacin da ya garzaya kan hanyarsu a garin Madiya.

Sai dai ya ce daga baya maharan sun sako Gana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here