Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamnan Jihar Ribas da mataimakinsa da kuma ɗauƙacin ’yan majalisar dokokin jihar tare da ayyana dokar ta-baci.
Shugaban na Nijeriya ya ce ya yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen sanya wannan doka wacce ta kwace mulkin jihar daga hannun gwamnan har sai lamura sun dawo daidai a jihar