Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihohi hudu da su fara shirye-shiryen hawan Bikin Sallah domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah.
Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan taron buɗa baki da sarakunan suka gudanar a dakin taro dake gidan gwamnatin Kano ranar Talata.
A cewar sanarwar, gwamna Yusuf ya jaddada cewa al’ummar jihar na bukatar kallon al’adar su lokacin da suka sanya sabbin tufafi a ranar Sallah, tare da yin jerin gwano don shaida sarakunan su a kan doki, da kuma yin musabaha.
Don haka, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, kuma ba za ta bari wasu gungun makiya su tauye wa ‘yan kasa wannan hakki ba.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa dukkanin hukumomin tsaro a jihar za su ba da himma wajen samar da kariya ga jama’a a yayin bikin.
Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cewa za a kaddamar da Majalisar Masarautar Jihar Kano a watan Afrilun bana domin samun damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
SolaceBase ta rahoto cewa gwamnan ya kara bayyana cewa za a sanar da ka’idojin majalisar, da’a, da sauran muhimman abubuwan da suka shafi majalisar a ranar kaddamarwar.
Ya yabawa sarakunan bisa irin himma da kyakkyawar alaka da suka nuna tun bayan nada su, inda ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar da ake samun kyakykyawar alaka a tsakanin sarakunan musamman ta fuskar matsayi.
Da yake mayar da martani, Shugaban Majalisar Masarautar Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar da cewa alakar da ke tsakaninsa da sarakunan masu daraja ta biyu abu ne na musamman.
Ya yi kira ga Gwamna Yusuf da ya yi amfani da cibiyoyin gargajiya don yada manufofi da tsare-tsare yadda ya kamata ga al’umma, tare da tabbatar da aiwatar da su cikin inganci.
A nasu bangaren, Sarkin Karaye, Muhammad Muhammad Maharaz; Sarkin Rano, Amb. Muhammad Isa Umaru; da mai martaba Sarkin Gaya Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir a madadin jama’arsu, sun nuna jin dadinsu ga Gwamna Yusuf bisa samar da takin zamani da samar da ababen more rayuwa a fannonin ilimi, lafiya da hanyoyin sadarwa a yankunansu.