Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta soki matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na ayyana dokar ta baci da kuma tsige gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN) ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce shugaban kasar ba shi da ikon tsige zababben gwamna a karkashin dokar ta-baci.
Don haka NBA ta bukaci Majalisar Dokoki ta kasa da ta yi watsi da duk wani yunkuri na amincewa da tsige Gwamnan Jihar Ribas da sauran zababbun jami’an da aka cire ba bisa ka’ida ba.
SolaceBase ta bayar da rahoton cewa NBA ta yi gargadin cewa dakatar da zababbun jami’an da ke karkashin dokar ta-baci ya kafa wani misali mai hadari da zai gurgunta mulkin dimokaradiyya kuma za a iya amfani da irin sa wajen tsige zababbun gwamnatoci a nan gaba.
Karanta: Ku fara shirye-shiryen hawan bikin sallah – Gwamnan Kano ga sarakuna
Kungiyar ta kuma bukaci duk wani mataki da aka dauka a jihar Rivers ya bi ka’idojin tsarin mulki da kuma ka’idojin dimokaradiyyar Najeriya tare da karfafa gwiwar masu ruwa da tsaki da suka hada da bangaren shari’a, kungiyoyin farar hula, da kasashen duniya, da su sanya ido sosai kan lamarin don hana gudanar da mulki da bai dace ba da kuma amfani da mulkin kama karya.













































