Jam’iyyar ADC ta yi Allah-wadai da yafiyar shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ya bai wa mutane 175 ciki har da masu laifin fataucin da safarar miyagun ƙwayoyi, tana cewa hakan babban abin kunya ne ga ƙasa.
Jam’iyyar ta bayyana cewa wannan mataki daga Tinubu da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na nufin sauya ma’aunin ɗabi’a da gaskiya a Najeriya, ta hanyar yin sassauci ga masu aikata manyan laifuka.
A cikin sanarwar da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi a birnin Abuja, ADC ta ce yafiyar na nuna rashin kulawa da ƙoƙarin da hukumomin yaƙi da miyagun ƙwayoyi ke yi, tare da bata sunan Najeriya a idon duniya.
Jam’iyyar ta ce ba da yafiya ga masu fataucin miyagun ƙwayoyi, masu safarar makamai, da masu laifin kisa, da’awar cewa sun nuna nadama ko sun koyi sana’a, babbar barazana ce ga tsarin adalci.
Ta ce yawancin waɗanda aka yi wa yafiya sun shafe ƙasa da shekaru biyu a gidan yari, alhali laifukan da suka aikata na ɗauke da hukuncin daurin rai-da-rai.
ADC ta bayyana cewa Najeriya na fuskantar mummunar matsalar amfani da miyagun ƙwayoyi musamman a tsakanin matasa, inda kididdiga ke nuna cewa kaso 14.4 cikin ɗari na al’umma na amfani da su, fiye da sau uku na matsakaicin kashi na duniya wanda yake 5.5 cikin ɗari.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa hukumomin kamar hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) da sauran jami’an tsaro suna sadaukar da rayukansu wajen yakar wannan matsala, amma wannan yafiya na Tinubu na rage darajar ƙoƙarinsu da kuma tsananta shakku daga ƙasashen waje kan jajircewar Najeriya wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi.
ADC ta kammala da cewa wannan lamari ya zama abin takaici ga ƙasa, yana kuma nuna cewa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu da jam’iyyar APC, komai yana tafiya bisa son rai, babu ladabtarwa, babu gaskiya, kuma an maye gurbin hukunci da rashin adalci.













































