INEC Ta Karawa Jami’ai 1,731 Girma

INEC Yakubu
INEC Yakubu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta amince da karin girma ga jami’ai 1,73 da suka yi hazaka a jarrabawar karin girma da aka yi a shekarar 2024.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Talata, wanda Daraktar wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri’a, Mrs Adenike Tadese, ta fitar a Abuja ranar Talata.

Tadese ya ce atisayen ya nuna wani muhimmin mataki da ke nuna jajircewar INEC wajen inganta jin dadin ma’aikata da kuma tallafa wa ci gaban aikin su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here